ABNA24 : Zarif ya bayyana haka ne a wata hira da ta hada shi da wata jarida da harshen farisanci a nan birnin Tehran.
Gwamnatin kasar Iran dai tana bin kasar Britania bashin Dalar Amurka fiye da miliyon 400 na kudaden makaman da ta sayarwa gwamnatin sarki sha amma bata bada makaman ba.
Zarif ya ce jan kafan da gwamnatin kasar ta Burtaniya ta ke yi na sakin wadannan kudade, su na da dangantaka da sakin Nazani wacce take cin kaso na shekaru biyar a halin yanzu saboda aikin samarwa tashar talabijin ta BCC Farsi ma’aikata a nan kasar Iran da ta yi. Bbc Farsi dai tana nuna matukar kiyayya da gwamnatin Iran.
An kama nazanin ne a shekara ta 2016 a lokacinda take kokarin shiga jirgi zuwa kasar Burtaniya daga nan Tehran.
342/